On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kotu Ta Yankewa ‘Dan Garkuwa Da Mutane Hamisu Bala Wadume Hukuncin Daurin Shekara 7 A Gidan Gyaran Hali

An yanke wa sanannen wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.

 

Mai shari’a Binta Nyako ta samu Wadume da laifin tserewa daga hannun hukuma da kuma yin mu’amala da muggan makamai ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a Nyako ta kuma yankewa Rayyanu Abdul hukuncin daurin shekara uku saboda ya ajiye Wadume a gidansa da ke Kano bayan Wadume ya tsere daga hannun ‘yan sanda a Ibi.

Alkalin kotun ta soke tuhuma 1, inda ake tuhumar Wadume da laifin yin garkuwa da Usman Garba wanda aka fi sani da Mayo da kuma karbar Naira miliyan 106 kafin a sake shi.

Mai shari’a Nyako, ta yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Yulin bana, inda jaridar Nation ta samu cikakken bayani a ranar Lahadi.