On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Kotu Ta Yanke Hukuncin Daurin Shekara 52 Ga Tsohon Hadimin Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan

Tsohon babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Doyin Okupe, a yammacin ranar Litinin, ya biya Naira miliyan 13 domin fansar kansa amadadin zaman gidan gyaran hali  na shekara 52 da aka yanke masa hukunci bisa laifin almundahanar kudi Naira miliyan 240.

Idan za’a iya  tuna mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta samu Okupe da laifuka 26 daga cikin tuhume-tuhume 59 da Hukumar EFCC ke yi a kansa.

Mai shari’a Ojukwu ta bayar da umarnin cewa tuhume-tuhume 26 da suka jawo hukuncin daurin shekara 2 kowanne, za su kasance a lokaci guda, ma’ana wanda ake tuhumar zai shafe shekaru biyu ne jimullah a gidan yari.

Sai dai mai shari’ar ta  bayar da zabin biyan Naira dubu dari  500  akan kowacce tuhuma daga cikin tuhume-tuhumen, wanda ya kai Naira miliyan 13, kuma dole ne sai an biya kafin karfe 4:30 na yammacin jiya Litinin.

Ta bada umarnin cewa idan Okupe ya gaza cika zabin tarar a cikin wa'adin, to a kai shi gidan yari na Kuje.

Sai dai binciken da aka yi a kotun da karfe 6 na yamma ya nuna cewa Okupe, wanda shi ne Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa ta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour  Peter Obi, ya biya kudin tarar.