Wata Babbar kotun Majistare dake nan Kano, Ta umarci Mataimakin babban sufeton yansanda mai kula da shiyya ta 1 dake nan Kano, daya gudanar da bincike na tsanaki akan zargin cin zarafin wani Dan jarida, da ake yiwa Dan majalisar wakilai dake wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhasan Ado Doguwa.
Umarnin da kotun ta bayar, ya biyo bayan ‘korafin da wakilin jaridar Leadership, Abdullahi Yakubu ya shigar gabanta, ta hannun lauyansa Bashir Umar.
A cikin wasikar da aka aikewa mataimakin sufeton yansandan mai kula da shiyya ta daya, dauke da kwananan wata 1 ga watan da muke ciki, Dan jarida Abdullahi Yakubu, ya zargin Dan majalisar da mangarinsa kunnensa na dama.
Dan jaridar ya kara da cewa, lamarin ya faru ne a gidan Alhasan Ado Doguwa, a lokacin da yake tare da abokan aikinsa da suka je domin samun karin haske kan abunda ya faru tsakanin Dan majalisar da kuma dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano Murtala Sule Garo.