Kotun Ma'aikata ta kasa ta Umarci Kungiyar ASUU Ta Janye yajin aikin da take kan yi, Wanda a yanzu haka yake cikin wata na 7 da somawa.
Mai shari'a Polycarp Hamman na babbar kotun taraiyya dake Abuja, ya Umarci Kungiyar malaman jami'oi ta kasa ASUU data janye aikin da ya Kai watanni 7 tana kan yi.
Bayan da alkalin kotun ya saurari lauyoyin gwamnati da Kuma na ASUU ya umarci malaman jami'ar dasu koma Aji domin cigaba da aikin koyarwa.
A ranar Litinin ne kotun ta jingine zartar da hukunci kan bukatar da gwamnati ta shigar inda take neman Malaman jami'oin su koma bakin aiki.
Tun ranar 14 ga watan fabarairun bana ne, Kungiyar ta soma yajin aiki, domin matsa lamba kan biya mata bukatunta, wanda suka hada da inganta kudin tafiyar da jami'oin sai Kuma Karin Albashi da sauransu.
Sai dai duk ganawar da aka sha yi tsakanin bangarorin biyu domin lalubo bakin zaren abun ya ci tura