Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar umartar hukumar zabe ta kasa INEC da ta dawo ci gaba da gudanar da rajistar masu kada kuri’a.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya ki amincewa da bukatar a jiya a bisa hujjar cewa kwanaki kalilan ne suka rage na yin rijistar kamar yadda doka ta tanada.
Alkalin ya ce zuwa ranar yanke hukuncin, babu kwanaki masu yawa fin a kai lokacin da kwanaki 90 zasu ragewa INEC ta gudanar da babban zabe.
Wadanda suka kai karar INEC sun hada da Anajat Salmat da Earnest Stanley da Cif Charles Okafor da Mista Samuel Oluwakemi.
Sun bukaci kotun da ta umurci INEC da ta dawo cigaba da rajistar masu kada kuri’a wadda ta dakatar kwanaki 208 kafin zaben 2023.
A farkon korafin da suka gabatar a gaban kotun, masu shigar da kara sun ce lokaci bai yi ba da INEC zata dakatar da cigaba da rajistar katin zabe sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Sun bukaci kotun da ta umarci hukumar zaben da ta gaba da gudanar da aikin rajistar kamar yadda dokar kasa ta tanada.