On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Kotu Ta Umarci Hukumar DSS Ta Gaggauta Gurfanar Da Emefiele

Wata babbar kotu dake zaman ta a Abuja ta umarci hukumar tsaro ta farin kaya DSS data kai tsohon gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele kotu idan har tana tuhumar sa da aikata wani laifi. 

Mai shari’a Hamza Mu’az yace a saki tsohon gwamnan babban bankin kasar a matsayin beli idan har ba’a shigar dashi kara a gaban kotu ba a cikin mako guda.

A ranar 9 ga watan yuni, shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele tare da bukatar shi daya miga ragamar shugabancin banking a Folashodun Adebisi Shonubi wanda ya kasance mataimakin gwamnan bankin.

Mai shari’a Mu’azu ya kara da cewa baa zai yuwu a ajiye dakataccen gwamnan babban bankin kasar a tsare ba ba tare da an tuhume shi da aikata wani laifi ba, yana mai cewa hukumar DSS bazata iya nemo hujoji akan Emefiele ba a lokacin da take tsare dashi ba.