Kotun ma’aikata ta kasa da ke zamanta a Kano a ranar Litinin ta umarci gwamnatin jihar Kano da ta mayar da Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin shugaban hukumar karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa.
Kotun tabada wannan umarni har zuwa lokacin da za’a yanke hukuncin kan karar daya shigar.
Rimingado yana kalubalantar sahihancin matakin da gwamnati ta dauka na sallamar sa ba tare da yin adalci ba.
Idan za a tuna a ranar 14 ga Disamba na 2022, kotun ta bayyana Rimingado a matsayin shugaban hukumar ta kuma umurci Gwamna AbdullahiGanduje da ya biya shi bashin albashi da ya haura Naira milliyan 5.
Amma a maimakon aiwatar da umarnin, gwamnatin jihar a ranar 24 ga Janairu na 2023 ta kori Rimingado, wanda tunda farkota fara dakatarwa, bisa dalilin kudurin majalisar dokokin jihar Kano a ranar 26 ga Yuli na shekarar 2022.