Wata babbar kotu mai lamba 17 dake zamanta a Miller Road karkashin mai shari’a Ado Ma’aji ta Umarci Ofishin jakadancin kasar Sin, Da ya samo wanda zai yiwa Bacanishen nan da ake zargi da halaka Ummukulsum Sani Buhari, Kisan gilla, Wanda zai yi masa tafinta a gaban kotu.
A lokacin da aka cigaba da zaman kotun a yau, Wanda ake tuhumar ya baiyana gaban kotun tare da lauyansa, Barrister Balarabe Muhammad Dan Azumi, Ya bukaci kotun da ta samar da wanda zi yiwa Bacanishen tafinta daga harshen turanci zuwa Sinanci, bisa ga dogaro da sashi na 36, 6 cikin baka da A Sai B da E na kundin tsarin mulkin kasa sashi na 237, 2 cikin baka na dokar aikatar Lefuka.
Kazalika shima babban lauyan gwmanati, kuma kwamishinan shari’a Barrister Musa Abdullahi Lawal, Yace duk da kasancewar Lauyan wanda ake kara ya bukaci samun tafinta akan lamarin, amma a baya, wanda ake tuhumar yayi magana da turanci a zaman kotun na baya, Inda yace zasu rubutawa ofishin jakadancin kasar China dake nan Najeriya wasika domin samar da wanda zai yi masa tafintar kafin nan da makwanni ukku lokacin da kotun zata sake yin zama.
Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya, Ya labarta mana cewa, Mai shari’a Ma’aji ya dage zaman kotun zuwa ranar 27 ga watan Octoban da muke ciki, Sannan kuma ya bada umarnin cigaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.