Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, Ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin halastacen dan takarar sanatan Yobe ta Arewa, a karkashin jam’iyyar APC.
Kotun ta goyi bayan hukuncin da kotun daukaka kara dake zamanta a birnin Damaturun jihar Yobe ta yanke tun a lokacin baya, wanda ta baiyana cewar, shugaban majalisar dattawa sanata Ahmad Lawan, ba shine halastaccen dan takarar jam’iyyar APC akan matsayin ba.
Kotun daukaka Karar ta baiyana cewa, kasancewar Sanata Ahmad Lawan bai shiga zaben fidda gwani na dan takarar sanatan da aka yi a ranar 28 ga watan Mayun bana, a saboda haka ba halastaccen dan takara ba ne.
Kotun mai alkalai Ukku, karkashin mai shari’a Monica Dongban Mensem , Ta baiyana cewa, zaben fidda dan takarar sanata da jam’iyyar APC ta kara yi a ranar 9 ga watan Yunin bana, haramtacce ne kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.