Reshen wata kotun daukaka Kara dake zamanta a Abuja, ta jingine hukuncin da wata babbar kotun taraiyya tayi, wanda ta aiyana Sanata Godswill Akpabio a matsayin halastaccen dan takarar sanatan Akwa Ibom ta Arewa karkashin jam’iyyar APC.
Kotun mai Alkalai Ukku, Mai shari’a Danlami Senchi ne ya karanta hukuncin da kotun ta yanke a ranar Litinin, Inda ya baiyana cewa, Sanata Godswill Akpabio, ya gaza gabatar da kwararan hujjojin da suka dace kan kasancewarsa a matsayin, bisa ga tanadin doka.
A saboda haka ne, Alkalan kotun suka baiyana cewa, Kasancewar Godswill Akpabio ya nemi zama dan takarar shugabancin kasar nan karkashin jam’iyyar APC, bai samu damar shiga zaben fidda gwani na kujerar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa ba, wanda hukumar Zabe ta kasa ta sanya ido a kansa ranar 27 ga watan Mayun Bana, kuma har ta kaiga an aiyana Udom Ekpoudom a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kotun daukakar karar, ta jingine hukuncin da babbar kotun taraiyyar dake zamanta a Abuja tayi a ranar 22 ga watan Satumbar da ya gabata, inda ta bukaci hukumar INEC ta gaggauta saka Akpabio a matsayin halastacen dan takarar sanatan Akwa Ibom ta arewa a karkashin jam’iyyar APC.