Kotun sauraren kararrakin zabe dake zamanta a birnin Lokoja, Ta sauke shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da aiyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa, Sanata Jibrin Isah daga kan kujerarsa ta sanata, Bayan data soke sakamakon zabe na rumfunan zabe 94 da suke a shiyyar da yake wakilta.
A yanzu haka mai shari’a K.A Orjiako, Ya umarci hukumar zabe ta kasa ta gaggauta janye shaidar cin zabe data baiwa sanatan, Sannan ta sake gudanar da zaben cike gibi a rumfunan zabe da abun ya shafa.
Dan takarar jam’iyyar PDP, Dr Victor Adoji ne ya shigar da kara gaban kotun, inda yake kalubalantar nasarar da Sanata Isah ya samu, bisa ikirarin cewar an soke sakamakon zabe a wasu akwatinan zabe da aka samu aringizon masu kada kuri’a.
A hukuncin da alkalin kotun ya yanke ya amince da dukkanin wasu shaidu da mai kara ya shigar gaban kotun.
Sanata Isa dan shekara 63 a duniya ya kasance tsohon dan siyasa, Kuma shine wanda aka gani ya durkusawa Gwamna Yahya Bello na jihar Kogi ya bashi hakuri, kamar yadda aka nadi bidiyon nasa ta cikin wata kyamara.