On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Kotu Ta Rufe Kamfanin Sarrafa 'Karfe Na 'Yan China A Kano Kan Karya Dokar Tsaftar Muhalli

Kotun tafi da gidanka kan tsaftar muhalli ta karshen Wata a Kano ta bada Umarnin rufe kamfanin Youngxing ba tare da bata lokaci ba da kuma tarar naira milliyan 5 saboda bijirewa dokar tsaftar muhalli da jefa kananan ma'aikata cikin hatsari.

Da yake yanke gurfanar da kamfanin a gaban mai shari'a Auwal Yusuf Sulaiman, shugaban kwamitin karta kwana akan tsaftar muhalli Dr Kabiru Ibrahim Getso, ya bayyana takaicinsa akan yadda kamfanin na 'yan Kasar China ya bude ayyukansa a yau asabar da aka ware awanni 3 domin tsaftar muhalli ga luma rashin tsafta a harabar kamfanin.

Getso ya nunar da cewa an samu labarin kamfanin dake titin wajen gari ta gabashin kwaryar birni ya yi kaurin suna wajen bijirewa dokokin Jihar Kano wanda ko a lokacin dokar kulla ta Corona sun ki tsayar da ayyukansu yanayin da acewar  kwamishinan ba za'a lamunta ba.

Da yake yanke hukuncin mai shari'a Auwal, yace an samu kamfanin da gudanar da aiki kafin karfe 10 na safe saboda haka ya bada Umarnin kullewa da biyan tarar kuɗi.

Bayan kamma hukuncin Dr Getso yace wajibi ne kamfanin ya biya tarar sannan ya Samar da matakan kariya ga ma'ikata inda za'a tura tawaga ta tabbatar da aiwatar da matakan.

Har ila yau an wata kotun ta tafi da gidanka ta rufe gidan mai na Mam  dake kan babban  titin wajen gari na yammacin kwaryar birni tare da cin tarar naira dubu dari biyar (500,000)

Wakilinmu Nura Haruna Mudi ya rawaito cewa rahota  jumillah wadanda suka karya dokar tsaftar muhalli a wannan wata kuma aka gurfanar da su tare da yanke mu su hukunci sun kai 58 inda zasu biya tarar kuɗi Naira milliyan biyar da dubu dari 5 da tamanin da bakwai (5,587,000).