Kotu ta baiwa Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC damar mallake wasu gine-gine har guda 324 mallakin hukumar fansho ta jihar Kano.
Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun taraiyya dake Abuja shi ne ya bada umarnin mallake gine-ginen. ga hukumar EFCC,kamar yadda kakakinta Wilson Uwujaren ya baiyaan ta cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba.
Kadarorin dai sun kunshi rukunin gidaje na sheik Jafar Mahmud Adam guda 168 wanda aka fi sani da Bandirawo City da Sheik Nasiru Kabara wanda aka fi sani da Amana City sai kuma rukunin gidaje na sheik Khalifa Ishaq Rabiu city.
Idan ba’a manta ba,Yan fansho sun zargi tsohon gwamnan jihar kano Rabiu Musa Kwankwaso da yin amfani da kudinsu wajen gina gidajen.