Kotun sauraren kararakin zaben shugaban kasa ta jingine hukunci akan karar da dan takarar shugaban kasa na jamiyyar PDP Atiku Abubakar ya shigar inda yake kalubalantar nasarar da shugaban kasa Bola Tinubu na jamiyyar APC ya samu.
Kotun karkashin jagorancin masu sharia guda biyar wadanda mai sharia Haruna Tsamanni ke shugabanta ta jingine hukunci zuwa wani lokaci da za’a sanar da wadanda abin ya shafa nan gaba.
Atiku wanda ya rike matakin mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1999 zuwa 2007 ya halarci zaman kotun na ranar Talata 1 ga watan Agusta 2023.
Masu karar jamiyyar PDP da kuma na Labour day an takararsu na bukatar a soke aiyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekarar.