Babbar Kotun taraiyya dake zamanta a Abuja ta bada umarnin tsare dakataccen babban akanta na kasa, Ahmed Idris a gidan gyaran hali.
Daukar matakin ya biyo bayan gurfanar dashi da Hukumar EFCC tayi a gaban kotu bisa zarginsa da karkatar da wasu makudan kudade wanda yawansu ya kai naira bilyan Dari da Tara da Milyan 400.
An gurfanar dashi ne a gaban kotu bisa tuhumarsa da aikata lefuka 14, wanda suka hada da baki da kuma cin amana da kuma yin wadaka da baitul malin gwamnati.
Mai shari’a A O Adeyemi Ajayi ya bada umarni tsare ahmed Idris da sauran mutanen da ake tuhuma a gidan gyran hali har zuwa ranar larabar Makon Gobe, lokacin da za’a saurari bukatar bada shi beli.