Wata babbar kotun jihar Benue dake zamanta a birnin Makurdi, Ta haramtawa shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sanata Iyorchia Ayu, Cigaba da baiyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Daukar matakin ya biyo bayan wata kara da aka shigar gaban kotun akan shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Inda kuma kotun ta dage zamanta zuwa ranar 17 ga watan gobe domin cigaba da zaman shari’ar.
Da yake yiwa manema Labarai jawabi a birnin Makurdi, Mai shigar da karar, Mister Terhinde Utaan,Ya ce saboda matakin da shugabannin jam’iyyar PDP a mazabar shugaban jam’iyyar suka dauka na dakatar dashi, ba daidai ba ne ya cigaba da rike matsayin shugabancin jam’iyyar, wanda hakan zai haddasa samun rashin hadin kai a tsakanin jam’iyyar.