Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta hana hukumar yaki da rashawa ta EFCC da hukumar ‘Da’ar ma’aikata da kuma hukumar yaki da rashawa ta ICPC shiga harkokin hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano.
Idan za’a iya tunawa EFCC da CCB sun rubuta wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano wasika inda suka bukaci gudanar da bincike akan ayyukanta da na shugabanta Barista Muhuyi Magaji Rimingado.
A wani umarni da ya bayar a ranar Litinin mai shari’a Farouk Lawan Adamu, ya ce umarnin ya hana EFCC da CCB da ICPC kamawa ko tsoma baki cikin harkokin duk wani ma’aikaci ko wani da ke karkashin ayyukan masu shigar da kara.
Daga nan ne kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Satumba 2023.