Wata babbar kotun taraiyya dake zamanta a Abuja ta hana gwamnan jihar kano, Abba Kabir Yusuf daukar kowane irin mataki na kamawa ko tsare, Dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Alhasan Ado Doguwa,har sai bayan kotun ta kammala zaman karar da aka shigar gabanta.
Mai shari’a Donatus Okorowo shi ne ya bada wannan umarni biyo bayan bukatar da Lauyan Alhasan Ado Doguwa, Afam Osigwe SAN ya shigar gaban kotun.
Lauyan Alhasan Ado Doguwa ya shigar da kara gaban kotun,Yana neman ta baiwa dan majalisar kariya, saboda zargin gwamnatin kano da yunkurin sawa a kama shi tare da tsare, bisa zargin da ake masa da hannu wajen tada zauni tsaye a zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar dokokin taraiyya.
Mai shari’a Okorowa ya umarci dukkanin bangarorin biyu da kowa ya tsaya kan matsayinsa cak, har zuwa lokacin da kotun zata kammala zamanta akan shari’ar.