![](https://mmo.aiircdn.com/370/639ac7f1f3fda.jpg)
Shin kana daya daga cikin mutanen dake tsammanin babban bankin kasa CBN zai kara lokacin yin amfani da tsaffin kudi, yan naira 200 da 500 da kuma Dubu 1, bayan karewar wa’adin ranar 10 ga watan da muke ciki da bankin ya bayar? To idan har haka ne ya kamata ka sake yin karatun ta nutsu domin yin abunda ya kamata kafin kurewar lokaci.
Hakan ya biyo bayan yadda wasu jam’iyyun siyasa guda hudu, suka samu wani umarni na wucin gadi daga wata babbar kotun taraiyya wadda ta hana Babban bankin kasar kara lokaci kan yin amfani da tsaffin kudin, daga bayan ranar 10 ga watan da muke ciki na Fabarairu.
Jam’iyyun sun hada da A A Sai A P P Da A P M Da kuma jam’iyyar NSM.
Kotun ta bada umarnin hana babban bankin kasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran bankunan kasuwanci 27 daga cigaba da yin amfani da tsaffin kudin, daga bayan ranar 10 ga watan da muke ciki.