Wata reshen Kotun Daukaka Kara dake zamanta a birnin Ikko, Ta yankewa Sanata Peter Nwaoboshi Mai wakiltar Delta ta Arewa,a majalisar dattawa, hukuncin daurin shekara 7 a gidan gyaran hali.
Kazalika Kotun ta umarci a rufe wasu kanfanoninsa biyu, wanda suka hada da Golden Touch Construction Project Ltd da Suiming Electrical ltd , kamar yadda yake bisa sashi na 22 na dokara yaki da aikata almundahanar kudi ta shekarar 2021.
Yanke hukuncin ya biyo bayan karar da Hukumar EFCC ta daukaka a gaban kotun, inda take kalubalantar hukuncin da mai shari’a chukwujekwu Aneke na Babbar kotun taraiyya ya yanke a ranar 18 ga watan yuni, inda ya wanke tare da sallamar wanda ake kara kan wasu tuhume-tuhume biyu da suka danganci aikaya almundahanar kudi.