Wata babbar kotun shari'ar musulunci dake zamanta a nan Kano, ta datse igiyar auren Asiya Abdullahi Umar Ganduje da Maigidanta Inuwa Uba, ta hanyar yin Khul'i a tsakaninsu.
Asiya Ganduje wadda ta kasance 'yar gwamnan jihar Kano, ta garzaya kotun ta hannun lauyanta, inda take neman kotun ta kawo karshen auren dake tsakaninta da mijinta, inda ta baiyana cewar zata mayar masa da sadakin da ya bata naira dubu hamsin.
Da yake yanke hukuncin, Mai shari'a Mallam Abdullahi Halliru, Ya ce hujjojin da aka gabatar a zaman shari'ar sun tabbatar da cewar mai karar ta karbi naira dubu hamsin.
Sai dai a nasa bangaren Lauyan wanda ake kara, Umar I Umar, Ya yi fatan kotun zata bashi dukkanin wasu bayanai na yadda zaman kotun ya kasance, inda ya ce yana da sha'awar zasu daukaka kara zuwa kotun sama, bayan sun tattauna da wanda yake karewa Inuwa Uba.
A hirarsa da wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya, Lauyan mai kara, Barister Ibrahim Aliyu Nasarawa, Ya ce kotun ta raba auren ne bisa tsarin shari'ar musulunci.