A yayin da ake tsaka da zanga-zangar halin tsi-tsi a kasar nan, A yanzu haka wata Babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas ta amince da wata bukata, wadda ke neman ‘kayyade farashin kayayyaki a kasar nan, nan da kwanaki bakwai masu zuwa.
Mai shari’a Lewis Allagoa ne ya bayar da wannan umarni biyo bayan karar da lauyan nan mai rajin kare hakkin Dan adam, Femi Falana SAN ya shigar gaban kotun.
Falana ya maka ministan shari’a na kasa da Hukumar kayyade farashin kayayyaki gaban kotun, Inda yake neman ayi amfani da karfin dokar daidaita farashin kayayyaki ta kasa, domin kayadde farashin kayayyaki a Najeriya.
Bayan zaman kotun na jiya Laraba, Ta baiyana cewar kasancewar babu wanda ya soki da’awar mai ‘kara, a saboda haka ta amince da bukatar daidaita farashin kayayyaki a kasa.
Kotun ta umarci wadanda ake kara, dasu gaggauta ‘kayyade farashin kayayyaki kamar su Madara da Fulawa da Gishiri da Sukari da Keke sai Ashana da Babur da Motoci da farashin Man fetir da Kananzir da sauransu.