Wata Kotun Shari’ar Musulunci dake jihar Bauchi Ta yankewa wasu mutane Ukku Hukuncin Kisa ta hanyar jefewa, sakamakon cin zarafin wasu Kananan Yara maza biyu, bayan sun basu kayan maye.
Wani Jami’in Hukumar Hisba dake Jihar Bauchi, Adamu Dankafi Ya fadawa kotun dake Ningi Yadda Mutanen Ukku suka hada baki wajen aikata lefukan a lokacin da ake yi masu tambayoyi a gaban kotu.
Ya kuma kara da cewa, an kama mutanen ne a kauyen Gawada a cikin watan Mayun Bana sakamakaon Korafin da Iyayen yaran suka shigar na cewar mutanen sun bawa yaransu kayan maye.
Adamu Dan Kafi, Ya kara da cewa Mutanen masu shekaru 20 zuwa 70 basu samu wani lauya da zai kare suba a lokacin da aka gabatar da shari’ar, inda ya baiyana cewa suna da wa’adin wata Daya domin su daukaka kara.