Kotu a nan Kano ta bada umarnin cigaba da tsare Murja Ibrahim Kunya a gidan Gyaran Hali.
Kotun ta ce a cigaba da tsare ta har zuwa ranar 16 ga watan fabarairun da muke ciki, ina za'a dawo domin cigaba da zaman kotun.
Ana zarginta da yin kalaman rashin da'a wanda suka sabawa tarbiya da kuma yanayin zamantakewar al'umma.
Zauren malaman jihar Kano ne suka kai karar ta wata Kotun shari'ar musulunci dake garin Bichi a nan kano, Inda kuma 'yansanda suka dakume ta kamar yadda Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya ya ruwaito mana.