Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano a yau Alhamis ta tabbatar da Mohammad Sani Abacha amatsayin zababben dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kano
Alkalin kotun mai shari’a A.M Liman a wani hukunci da ya yanke a yammacin yau ya soke zaben fidda gwanin da ya tsaida Sadik Amunu Wali a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP tare da umartar INEC da ta maye gurbin sunansa da sunan Muhammad Sani Abacha.
Tunda farko an tsara yanke hukuncin ne da misalin karfe 12 na rana a yau amma daga baya aka canza zuwa karfe 4:00 na yamma.
Kotun ta amince da dukkan rokon wanda ya shigar da kara Mohammed Sani Abacha akan Sadik Aminu Wali da INEC da Kuma jam'iyyar PDP.