Wata kotu dake zaune a karamar Hukumar kura a jihar kano ta tisa keyar wata amarya da ta zubawa Abokiyar zamanta tare da ‘yarta mai shekara 4 a duniya Ruwan zafi.
Rahotanni sun baiyana cewa, Amaryar mai suna Maryam Abdurrahman Chiromawa ta aikata ‘Danayen aikin ne, a lokacin da kishiyar ta ta ke tsaka da bacci
Har ila yau, mai Laifin ta amsa Laifin da ake tuhumarta da aikatawa.
Wakilinmu Ado ‘Danladi Farin Gida ya rawaito alkalin Kotun Aminu Usman Fagge ya dage cigaba da shari’ar zuwa mako uku na gaba lokacin da ake fatan Matar da aka watsawa ruwan zafin zata smu sauki tare da diyarta.