On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kotu Na Dab Da Yankewa Sheik Abduljabbar Hukunci

Sheik Abduljabbar Nasir Kabara

A yau Alhamis ne, Mai shari'a Ibrahim Sarki Yola na Babbar kotun shari'ar Musulunci dake kofar Kudu a cikin birnin Kano, Ya kammala sauraren lauyoyin bangarorin biyu.

Babbar Kotun Shari'ar Musulunci dake Kofar Kudu Karkashin me Shari'a Ibrahim Sarki Yola ta ce za ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci kan karar da Gwamnatin Jahar Kano ta shigar da Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara bisa zarginsa da kalaman batanci.

Yayin zaman na Yau dukkannin bangarorin Shari'ar sun gabatar da Jawabansu na karshe ga Kotun a rubuce, wanda dama an sanya Yau domin karbar bayanan.

lauyan Gwamnati Farfesa Mamman Lawan Yusufari SAN ya roki Kotun data yi amfani da hujjojinsu ta yankewa Wanda ake kara hukunci dai dai da tanadin Shari'a

Kazalika Wanda ake kara Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara ya roki Kotun data yi amfani da Jawabansan ta Kori Karar da Gwamnatin ta shigar da shi, tare da umartarta ta ba shi hakuri.

Wakilinmu Bashir Faruk Durumin Iya ya labarta mana cewa Me Shari'a Ibrahim Sarki Yola ya ce Kotun za tai nazari kan Jawaban nasu ta Kuma ambaci ranar da za ta yanke hukunci nan da Makonni biyu masu zuwa