Jam’iyyar NNPP ta nesanta kanta da wasu dake Ikirarin ‘ya’yan jam’iyyar ne suna kalaman rashin amincewa da jagoran jam’iyyar na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa a karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta na kasa, Abba Kawu Ali, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar, Ladipo Johnson, ya ce an dade da korar wadanda suke kiran kan nasu amatsayin ‘ya’yan jam’iyyar ta NNPP.
A ranar Litinin dai Dr Agbo Major a Abuja ya shaidawa manema labarai cewa kotun karrakin zabe da kotun daukaka kara sun yanke hukuncin cewa gwamnan jihar Kano ba mamban jam’iyyar NNPP ba saboda rashin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Amma a cikin wani martani na gaggawa, Johnson ya bayyana ikirarin amatsayin Tuggu daga korarrun mambobin NNPP, kuma farfaganda.
Ya kara da cewa an dauki nauyinsu ne domin kawo rashin jituwa a cikin jam’iyyar.