Babban Bankin kasa CBN, ya ce da alama karancin takardun kudi da Naira da ake fuskanta a yanzu haka ya biyo bayan wasu makudan kudade da Bankunan ajiya suka kwashe daga rassa daban-daban na CBN.
Hakan na zuwa ne biyo bayan korafe-korafe da wasu abokan huldar bankuna suka yi kan karancin kudin da ake fuskanta na Naira a Na’urorin ATM da cibiyoyin POS da kuma kamfanonin Chanji.
Wata sanarwa da Sashen Sadarwa na bankin na CBN ya fitar a ranar Lahadi, ta ce shiga firgici da abokan huldar bankuna suka yi tare da cire kudi babu kakkautawa, shi ma wani bangare ne da ya haddasa karancin.
Sanarwar ta dage cewa akwai wadatattun takardun kudi.
Idan za’a iya tunawa dai babban bankin ya sanar da jama’a matakin tsawaita amfani da tsaffin takardun kudi na Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira dubu 1 a watan jiya.