Kamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na jihar Kano, farfesa Riskuwa Arabu Shehu, ya bayyana dalilan da suka sa aka ayyana zaben gwanan jihar Kano na shekarra 2019, a matsayin wanda bai kammala ba.
A wata ganawa da manema labarai a yau, ya bayyana rashin kammaluwar zaben a bisa dalilin yawan kuri’un da aka soke, sunfi yawan tazarar da manyan yan takarar biyu, Abba Yusuf na PDP, da Abdullahi Ganduje na APC, suka samu.
Da yake jawabi bayan shekaru 3 da yin zaben, Riskuwa yace ba’a dauki matakin ba ne domin ‘daga kafa ga jamiyya mai mulki, kamar yadda wasu ke zargi a jihar kano, sai dai kawai tsari ne da doka ta tanada.
A ranar 11 ga watan Maris na 2019, baturen zaben gwamnan jihar jihar farfesa Bello Shehu, ya bayyana sakamakon zaben gwamnan na karshe, a matsayin wanda bai kammala ba.