Kason farko na ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Sudan sun dawo gida Najeriya. An kwaso su ne ta cikin jirgi inda suka sauka filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja da karfe 11 da rabi na daren jiya.
‘Yan Najeriyar sun samu tarba ta musamman daga Ministar kula da harkokin Jin kai da kare afkuwar Bala’oi ta kasa,Sadiya Umar Faruk, sai shugabar Hukumar kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare, uwargida Abike Dabiri Erewa, da shugaban hukumar Ba da Agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ahmed Mustapha.
Da take yiwa mutanen jawabi, Ministar ta baiyana cewar za’a baiwa kowane mutum guda naira dubu 100 domin biyan wasu ‘yan bukatu da suka shafe su.
Ita ma a nata jawabin, Uwargida Dabiri Erewa ta baiyana cewar akwai ‘yan Najeriya kimanin milyan ukku a kasar Sudan, kuma gwamnati zata yi bakin kokarin domin ganin an kwashe su.
Rahotanni sun baiyana cewar a yanzu haka jiragin kanfanin Azman da na Max Air na kan hanyarsu ta zuwa kasar Masar domin kara kwaso ‘yan Najeriyar da suka yi gudun hijira daga kasar Sudan, saboda yakin da kasar ta samu kanta a ciki.