
Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta yammacin Afirka WEAC ta fitar da sakamakon jarabawar watan Mayu zuwa Yuni.
Yayinda aka fitar da sakamakon a jiya litinin, hukumar WEAC tace dalibai milliyan 1 da dubu dari 2 da 22 da 505 kwatankwacin kasha 76 da digo 36 na jimillar daliban sun samu nasara a darussa biyar ciki harda Turanci da Lissafi.
Wannan alkaluma sun nuna an samu koma baya da kasha biyar cikin dari idan aka kwatanta da kasha 81 da digo 7 da jimillar daliban da suka samu nasara a darussa biyar yayin jarabawar ta shekarar 2021.
Da yake sanar da sakamakon jarabawar jiya litinin a legas, shugaban hukiumar WEAC a Najeriya, Patrik Areghan yace an rike sakamakon dalibai dubu dari 3 da 65 da 564 sakamakon samunsu da laifuka masu alaka da satar jarabawa.