Kungiyar ma’aikatan dakunan karatu a Najeriya NLA ta bayyana damuwa akan rashin dakunan karatu a kashi 95 na makarantun gwamnati dake kasar
Shugaban kungiyar reshen Kano Mannir Abdullahi Kamba ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala makon dakin karatu da kungiyar ta shirya a Kano.
Yace manufar shirya makon ita ce wayar da kan jama’a kan mahimmancin dakin karatu da kuma bunkasa al’adar karatu a Najeriya da dawo da martabar dakunan karatu da suka bace a fadin kasar nan.
Yace a shekarun Alif 1980 a kowace Sakandare ko Firamare akwai dakunan karatu, amma a yanzu babu, saboda hala kungiyar ta sha alwashin dawo da martabar dakunan karatu a jihar Kano da ma kasa baki daya.
Yaci gaba da cewa, dalilai da dama ne suka haifar da durkushewar dakunan karatu da dabi’ar karatu a Najeriya, daga cikinsu akwai abubuwan da suka shafi siyasa da muhalli, da tattalin arziki da dai sauransu.
Haka kuma ya koka akan yadda ake karkatar da kason da doka ta tanadarwa dakunan karatu a kasafin kudin kowacce shekara wanda yace hakan na taka rawa wajen karuwar matsalar durkushewar bangaren.
Ya bukaci masu ruwa da tsaki su hada hannu wajen tallafawa harkokin karatu ga yara masu tasowa ta hanyar samar da Litattafai da za’a karanta da yanayi mai kyau da ware lokutan karatu na musamman da malamai masana dakunan karatu.