Hukumomin kasar Moroco sun amince sun amince da yin amfani da Tabar Wiwi a masana’antu da bangaren yin magani da kuma yin fataucin ta zuwa kasashen waje.
Hukumomi a kasar sun baiyana cewa Manoman da suke a matsayin kungiya a tsaunikan Al-Houciema da Taunat da Chefchauen dake arewacin kasar, za’a basu izinin noma Tabar wiwi domin ganin sun biya bukatun bangarori 10 da aka amince ayi amfani da ita.
Dama dai noman Tabar wiwi a kasar Moroco ta haramtacciyar hanya ba sabon bakon abu bane, sai dai a halin yanzu dokar da yan majalisar dookokin kasar suka amince da ita ta haramta yin amfani da Tabar Wiwi domin jin Dadin jiki kadai.
Dokar dai zata temaka wajen bunkasa kudin shiga da manoman ke samu da kuma kare su daga fadawa hannun dillalan miyagun kwayoyi wanda suke safarar Tabar wiwi ta haramtacciyar hanya zuwa nahiyar turai.