On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Kasafin 2022: Jihar Jigawa Ta Sake Zuwa Matsayi Na Farko A Jerin Jahohin Najeriya Kan Bayar Da Bayanan Kasafin Kudi - CIRDDOC

A karo na biyu Jihar Jigawa Jiha ta sake zama kan gaba wajen bayar da bayanan  kasafin Kudi na Jihohin Najeriya na shekarar 2022.

A cikin rahoton da cibiyar CIRDDOC  ta fitar, jihar ta jigawa ta  samu kashi 84 inda ta doke Kano da Adamawa da Ondo wadanda suka samu kashi 64; 63 da 61 a tsakanin sauran jihohi 32 da babban birnin tarayya Abuja.

Babban daraktan kungiyar bincike kan tattalin arziki da zamantakewa, Tijjani Abdulkarim, ya tabbatar da hakan a wajen taron kaddamar da rahoton bibiyar kasafin kudi na shiyyar Arewa maso yamma da aka gudanar a jihar Kano.

Tijjani wanda Muhammad Bello jami’in tattara bayanan kasafin kudi a Kano ya yi mafana amadadinsa da harshen hausa, yace an samu cigaba sosai idan aka kwatanta da shekarar 2015 saboda karancin bayanai.

Yace wayar da kai da kungiyoyi sukayi ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da kuma al’umma hakan ya taimaka wajen samar da cigaban da ake gani a yanzu.

Ya ce yanzu al’umma na bibiyar kasafin kudinsu a matakai daban-daban.

Bello ya kara da cewa abun a yaba ne yadda Kano ta zama jiha ta biyu idan akayi da la’akari da matakin da take ciki a baya.

Anasa bangaren, kwamishinan kasafi da tsare-tsare na Jihar Kano Musa Sulaiman Shanono, ya bada tabbacin cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf zata sauya fasalin yadda ake tsarawa da aiwatar da kasafin kudi ta hanyar shigar da al’umma da kumamasu ruwa da tsaki tun daga matakin farko.

Idan za’a iya tunawa, Binciken tafiyar da kasafin kudi na jahohin Najeriya na shekarar 2022 ya gabatar da batutuwan da suka shafi fayyace komaia bude, shigar da al’umma da  kuma sanin ya kamata a cikin kasafin kudi da tsarin siyan kayayyaki a matakin kananan hukumomi a Najeriya.

Rahoton ya nuna wasu sauye-sauye masu kyau ga jihohin da a yanzu ke wallafa  takardun kasafin su a shekarar 2022 idan aka kwatanta da shekarar  2020.

Duk da yake wani kyakkyawan ci gaba ne yadda a yanzu haka wasu jihohi na wallafa takardun kasafin kudinsu, bayanai sun nuna rashin daidaito yayin da wasu jihohin suka daina wallafa wasu takardu da aka wallafa a baya.

Dangane da irin takardun da Jihohi ke wallafawa, binciken ya nuna cewa fitar da takardun kasafin kuɗi na jihohi ya inganta a cikin 2022 idan aka kwatanta da 2020.

Ko da yake, bayanai sun nuna cewa wasu jihohi sun wallafa bayanan kasafin kuɗi a cikin 2022 fiye da na 2020,  ingancin bayanai a cikin takaddun da aka wallafa ba su samu matsakaicin maki ba.