Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, Ta ce ta cafke masu karya doka har dubu 3 da 245 daga farkon watan janairun bana zuwa Disambar da muke ciki.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a yau juma’a. Ya ce an samu raguwar masu aikata lefuka a bana, idan aka kwatanta dana shekarar data gabata, lokacin da jami’an hukumar suka dakume masu karya dokokin hanya dubu 7 da 835.
Sanarwar ta baiyana cewa, A bana, Hukumar Karota, ta samu nasarar yiwa baburan adaidaita sahu dubu 52 da 242 rijista.
Kazalika a majalisar dokokin jihar kano ta amince da dokar hukumar ta shekarar 2022 da aka yiwa gyaran fuska, wanda hakan zai bata damar yin aiyukanta cikin salama.