Karin wasu Yan Najeriya 143 da suka makale a kasar Libiya sun dawo gida a ranar Talata, inda suka sauka filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad dake birnin Ikko.
Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, Mustapha Ahmed ya baiyana cewa, an sauke mutanen da aka dawo dasu gidan ne ta filin tashi da saukar jiragen dakon kaya dake cikin filin jirgin saman.
Ahmed yace mutanen sun hada da Manyan mutane 96 Sai Kananan Yara 8 Da wani jariri 1 sai kuma manyan Mata 36 da kuma wata karamar yarinya tare da wata Jaririya.