Shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa Masu Zaman Kansu, Debo Ahmed, ya ce shirin kara farashin man fetur da dizal yana nan daram.
Kalaman nasa na zuwa ne a yayin da aka fara fuskantar dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai dake birnin Ikko da Abuja sakamakon karancin samar da man daga Kanfanin main a kasa NNPC.
A yayin wata hira da ya yi da manema labarai ya zargi masu rumbunan ajiyar mai dake zaman kansu da sayar da man sama da farashin da aka kayyade.
Yace akwai bukatar gwamnati ta binciki ayyukan masu rumbunan ajiyar mai domin gano inda gizo ke sakar.
Ahmed ya yi kira ga gwamnati da ta shigo da karin man fetur zuwa cikin kasar nan domin ceto kasar nan daga fuskantar matsalar karancin mai.