On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Karin Albashin Da Gwamnati Ta Yiwa Ma'aikata Ya Yi Kadan.

Dan Majalisar wakilai na Ghari da Tsanyawa

Injiniya Sani Bala Tsanyawa, ya ce a ra'yinsa karin Albashin ba zai wadaci Ma'aikata wajen gudanar da bukatunsu na yau da kullum.

Nan kuma engr Sani Bala ya ce karin Albashin da gwamnatin tarayya ta yi da kaso 25 zuwa 35 cikin 100 ga Ma'aikatan Kasar nan, ya yi matukar kadan.

Injiniya ya ce la'akari da bukatun yau da kullum da kuma tashin farashin kayayyaki, Karin da aka yiwa Ma'aikatan babu abunda zai yi masu.

A saboda haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sake yin nazari kan karin Albashin domin yin abunda ya dace, a hirarsa da Arewa radio, injiniya Sani Bala wanda shine shugaban kwamitin ma'aikata a Majalisar wakilai, ya ce la'akari da yanayin da kasa take ciki, Ma'aikacin gwamnati na bukatar samun gyara a Albashinsa.