Shugaban kungiyar masu sana’ar sayar da Dabbobi a birnin Calabar, Alhaji Isyaka Mohammed, Ya ce yana ware naira milyan daya cikin aljihunsa, domin bada cin hanci a shingayen binciken ababen hawa dake kan hanya, domin ganin an wuto masa da dabbobinsa da ya dauko daga yankin Arewacin kasar nan zuwa jihar Cross River dake kudancin kasar nan.
Mohammed ya baiyana haka ne ga manema Labarai, lokacin da yake tsokaci kan farashin Raguna a wannan lokacin da shagalin babbar sallah.
Shugaba, Ya yi zargin cewar an samu tashin farashin raguna ne, bawai saboda janye tallafin man fetir ba, sai dai kawai, saboda kudin nagoro da ake karba daga hannunsu akan hanya daga Arewa zuwa kudancin kasar nan.
Ya kuma kara da cewar manyan motocin dake daukar masu dabbobi daga Arewa zuwa kudu suna amfani ne da man dizal, wanda farashin ke cigaba da sauka sannu a hankali, a saboda haka babban kalubalen da suke fuskanta, shi ne yawan karbar nagoro daga hannunsu akan hanya.