Ana cigaba da fuskantar karancin tsabar kudi a babban birnin jihar Legas yayin da masu hulda da bankuna ke iya cirar naira dubu 10, inda wasu bankunan ba su da isassun kudi.
Hakan dai na faruwa ne duk da tabbacin da babban bankin kasa CBN ya bayar a makon da ya gabata kan ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi na Naira wajen hada-hadar kasuwanci.
Dangane da tsarin takaita amfani da tsabar kudi na babban bankin Najeriya, daidaikun abokan hulda na iya fitar da mafi yawan kudi naira Naira dubu dari 5 a kowane mako tare da kuma naira dubu 100 a rana guda, yayin da kamfanoni aka Takaita fitar da tsabar kudi zuwa Naira miliyan 5 duk mako.
Wasu daga cikin rassan bankunan sun bayyana cewa basu da isassun kudade yayin da sauran ke cewa suna jiran kudin daga babban banki.
………