Karancin iskar gas da ake dafa abinci ya addabi sassan jihar Legas da wasu jihohin kasar nan.
Sauran jihohin da abin ya shafa, kamar yadda rahotanni suka bayyana sun hada da, Katsina da Sokoto da Delta da Kaduna da Kano.
Tun a karshen watan da ya gabata ne aka lura da tashin farashin farashin makamashin.
Masu gidajen gas sun kara farashin da kashi 66 cikin dari a watan Oktoba kadai.