Kansiloli bakwai daga cikin 11 na karamar hukumar Ijebu-ta gabas a jihar Ogun sun dakatar da shugaban karamar hukumar Wale Adedayo na tsawon watanni 3, kwanaki bayan ya kai korafi ga hukumar EFCC da ICPC kan gwamnan jihar Dapo Abiodun.
Kansilolin sun sanar da dakatarwar ne a jiya, bisa zarge-zarge 15 da suka hada da cire Naira milliyan 4 daga asusun karamar hukumar a shekarar 2022 domin bada tallafi . Sun yi ikirarin cewa ba’a gudanar da shirin ba.
Idan dai za a iya tunawa Adedayo, a cikin wasikar da ya rubutawa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, ya koka kan rashin samun kason kananan hukumomi 20 na jihar tun daga shekarar 2021 daga gwamnatin jihar.
Sai dai a ranar Talata ne shugabannin kananan hukumomi 18 daga cikin 20 suka ziyarci gwamnan domin rokon afuwarsa game da kalaman Adedayo da wasikar da ya rubuta.
Da yake mayar da martani, Adedayo ya sha alwashin kalubalantar dakatarwar da aka yi masa a kotu, inda ya bayyana zargin da ake masa a matsayin maras tushe.
Ya yi iƙirarin cewa ba shi da damar shiga asusun karamar hukumar kuma ba za a iya ɗaukar irin waɗannan kuɗi, ba tare da bin ka'idoji ba.