On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Kano Zata Zama Cibiyar Bincike Da Cinikayar Namun Daji - MD KAZOWMA

Jami'ar Bayero Kano ta rattaba hannu akan wata yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar kula da abbobi da kuma gandun daji ta jihar Kano KAZOWMA domin habaka kiwon Namun daji.

Da yake jawabi a wajen bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar Litinin, Manajan daraktan hukumar KAZOWMA, Sadiq Kura Mohammed, ya ce za a yi amfani da hanyoyin kimiyya wajen kula da Namun daji da kuma sauran Itatuwa dake barzanar bacewa domin su yawaita.

Hon Kura Mohammed ya ci gaba da cewa kasancewarsa gidan namun daji mafi girma a yammacin Afirka, ya sanya hannu akan yarjejeniyar da jami'ar Bayero wadda za ta zama mai amfani ba ga jihar Kano kadai ba, har ma da daukacin nahiyar Afirka.

A nasa bangaren, shugaban jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce Jami’ar BUK ta amince ta hada gwiwa da KAZOWMA ta fannin musayar ma’aikata, da samar da rigakafin dabbobi, da gandun daji domin bayar da gudunmuwa wajen bincike da fagen Ilimi.

Ya kuma tabbatarwa da hukumar ta gida Zoo cewa  BUK a shirye take domin cigaba da haÉ—in gwiwa.