On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Kano Pillars Ta 'Dauki Kofin Share Fage Na Hadin Kan Kungiyoyin Arewa

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta zama zakara a Gasar Cin Kofin zaman Lafiya da hadin kan kungiyoyin Arewa domin share faggen shiga kakar wasanni ta bana da aka yi a Kano.

Gasar ta mako guda an fafata tsakanin kungiyoyi hudu da suka hada da, Kano Pillars da  Gombe United da  Katsina United da kuma kungiyoyin kwallon kafa na Neja Tornadoes.

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta zama zakara da maki bakwai a wasanni uku da ta buga, inda ta ci wasa biyu da canjaras daya.

Mai horas da ‘yan wasan sai masu gida, Abdu mai Kaba, yace akwai sauran aiki a gaban kungiyar kuma sun gano kura-kurai da za’a dauki matakan gyara.

Da yake sanar da rufe gasar a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar mata Kano da yammacin jiya Laraba, shugaban kwamitin wasanni na majalisar dokokin jihar Kano Alhaji Kabiru Dahiru ya taya kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars murna tare da bayyana wasan kwallon kafa a matsayin wani abu na hada kan al’ummar kasarnan.