On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Kano Na Cikin Jahohin Najeriya 6 Kan Gaba Wajen Fama Da Masu Tarin TB - Gwamnati

Gwamnatin jihar Kano ta ce jihar na ɗaya daga cikin jerin jahohi 6 da suka fi fama da cutar tarin fuka, inda a shekarar 2022 aka tabbatar da samun mutane 39,420 da suka kamu da cutar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf, shine ya bayyana haka a wani taron manema labarai jiya domin bikin ranar tarin fuka ta duniya na bana da Gwamnatin jihar Kano ta shirya da taimakon SMoH da SPHCDA tare da hadin gwiwar Breakthrough Action-Nigeria, ya ce gwamnatin jihar ta samu nasarar yiwa mutane sama da dubu 36  maganin cutar. 

Dakta Labaran ya kara da cewa, an samu nasarar hakan ne ta hanyar yin gwaje-gwaje da kuma maganin cutar tarin fuka kyauta a mazabu 484 da ke jihar tare da tabbatar da sakin kudaden shirin kula da masu cutar ta  TB  da na kuturta da nufin dakile yaduwar cutar.

Wakilinmu, Kamaluddeen Muhammad, ya rawaito kwamishinan na karawa da cewa  nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta habbaka wasu daga  cibiyoyin kiwon lafiya  matakin farko domin bunkasa ayyukan kiwon lafiya ga al'ummar jihar.