Kanfanonin jiragen sama na cikin gida da suka hada da Air Peace da Azman da Max Airn da kuma Aero sunki saka hannu kan yarjejeniyar dake tsakaninsu da hukumar aikin hajji ta kasa kan jigilar maniyyata aikin hajjin bana sakamakon rikicin da ake yi a kasar Sudan.
A yanzu haka an dage lokacin saka hannun kan yarjejeniyar zuwa ranar Talatar makon a yayin da wakilan kanfanonin jiragen saman suka nemi a basu lokaci domin tuntubar na gaba da su.
Sun yi ikirarin cewar Sararin samaniyar kasar Sudan wanda aka rufe shi saboda yakin da ake yi a kasar, zai shafi jigilar maniyyata aikin hajjin bana da suka taso daga yankin kasashen sahara, kasancewar dole ne sai an ratsa ta sararin samaniyar kasar kafin a shiga kasar saudiyya, muddin ba hanya aka sauya ba.
Sake yarjejeniya tsakanin kanfanonin jiragen saman da kuma Hukumar aikin hajji ta kasa zai sa dole sai dai a bi ta wata kasar maimakon ratsawa da sararin samaniyar sudan, wanda hakan zai kara yawan kudin aikin hajjin da Alhazai zasu biya.
A wani bangaren kuma wani kanfanin jirgin sama dan kasar waje na Fly Nas ya saka hannu kan yarjejeniyar jigilar Alhazan Najeriya dubu 28, wanda yake wakiltar kaso 40 bisa 100 na Alhazan da zasu je aikin hajjin bana.