Kanfanin Google da Netflix da kuma kanfanin sada zumunta na Facebook da sauran kamfanonin kasashen waje dake aiki a Najeriya sun biya sama da naira Tiriliyan 1 da bilyan 98 a matsayin haraji ga asusun gwamnatin tarayya cikin watanni 15 da suka gabata.
Adadin kudin ya kunshi duka Harajin Shigar da Kamfanonin ke samu da kuma Harajin kayyaki na VAT, Kamar yadda bayanan da hukumar kididdiga ta kasa ta fitar suka nuna.
A cewar Hukumar tara kudaden shiga ta kasa, Harajin kudin shiga da kanfanonin ke biya ya kai kashi 30 cikin 100 daga ribar da suke samu , Sai kuma harajin VAT da kanfanonin ke biyan kaso 7 da digo 5 cikin 100.
Tun da farko a shekarar 2020,An baiyana cewar, Gwamnatin Tarayya ta yi shirin kakaba haraji akan kanfanonin fasahar sadarwa na kasashen waje.