Kanfanin mai na kasa ya ce ba zai iya bada tabbacin cewar ba za’a samu dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai ba.
Shugaban kanfanin Mele Kyari wanda ya baiyana haka a ranar Talata, ya zargin cewar dogayen layukan ababen hawan da ake samu nada nasaba da yadda masu son cin riba a dare daya ke gudanar da harkokinsu.
A hirarsa da gidan Talabijin na kasa , Mele Kyari ya yi alkawarin cewar za’a samu saukin karancin man da ake samu daga makon gobe.
To sai dai kuma bai bada tabbacin cewar za’a karshen matsalar dogayen layukan ababen hawar nan bada jimawa ba.
Ya kara da cewa Najeriya na bukatar zunzurutun kudi har naira tiriliyan Hudu da bilyan 27 domin ta warware dukkanin wasu bukatu da suka shafi tallafin mai.