Kanfanin sarrafa Albarkatun mai na kasa NNPCL, Ya baiyana cewar matatar mai ta Dangote da ta Fatakwal da kuma sauran wadanda ake dasu, ba zasu sa a samu sauyin farashin man fetir ba.
Shugaban kanfanin, Mele Kyari ne ya baiyana haka, yayin wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na kasa, inda ya yi watsi da kalaman da ke cewar za’a samu saukar farashin man, kasancewar suma matatun zasu rika lissafin kudin da zasu kashe wajen aikin tace man, da sauran wasu batutuwa.
Ya kara da cewar matatar mai ta Fatakwal zata cigaba da aiki daga watan Disamba mai zuwa, sannan kuma duk tunanin da ake na samun saukin farashin man saboda man da Matatar mai ta Dangote zata rika tacewa, hakan ba zaisa farashin nasa ya sauka ba.
Kazalika ya tabbatar da cewar bayanan farashin mai na kowace jiha da aka ga yana yawo a shafukan sada zumunta, sun fito ne daga kanfanin man na kasa.